Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya ce rama kisan da aka yi wa mahifinsa kuma wanda ya riƙe muƙamin a gabansa, Ali Khamenei, “buƙatar ƙasa” ce kuma “dole ne ” a aiwatar da ita.
Kalaman sun fito ne cikin wani saƙon da aka gabatar yayin jana’izar marigayi Jagoran Addinin ƙasar, in ji kafar watsa labaran ƙasar IRIB.
“Mun sha alwashin rama zubar da jininka mara laifi da kuma na dukkan shahidai na yaƙe-yaƙe biyun nan daga masu kisan kai masu aikata laifuka mara matuncin,” kamar yadda Mojtaba Khamenei ya bayyana a cikin saƙon.
“Wannan lamarin ba ya dogara kan rayuwata ta kaina ko kuma kan sauran jami’ai . Ko muna nan ko ba ma nan, zai faru.”
An binne Ali Khamenei ranar Alhamis a wurin ibada na Imam Reza a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, lamarin da ya kawo ƙarshen mako ɗaya na gangamin jana’izarsa.
An kashe shi ne a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran da suka fara kaiwa ranar 28 ga watan Fabrairu kuma waɗanda hare-haren ramuwar gayyar Iran suka biyo bayansu.
Wani rahoton da jaridar The Wall Street Journal ta wallafa ranar Alhamis ta ce kwanan ne Isra’ila ta miƙa wa Amurka bayanan sirri da ke iƙirarin cewa Iran ta kitsa sabon shiri na kashe Shugaban Amurka Donald Trump.
A wani saƙon da ya wallafa ranar Jumma’a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, Trump ya yi barazanar ƙaddamar da hare-haren “dubban makamai masu linzami” kan Iran idan ta yi ƙoƙarin kashe shi.
A watan Yuni, Tehran da Washington sun rattaɓa hannu kan wata takardar fahimtar juna da Pakistan ta jagoranci samar da ita da zummar kawo ƙarshen yaƙin da aka fara a ƙarshen watan Fabrairu da kuma buɗe hanya ga yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa.
Takardar ta fahimtar juna ta yi kira ga kawo ƙarshen faɗa nan-take a dukkan fagen yaƙi da janye ƙawanyar sojin ruwa kan Iran da kuma sake buɗe mashigar ruwan Hormuz.
Duk da yarjejeniyar, ɓangarorin biyu sun yi musayar hare-hare a cikin wannan makon game da wucewar jiragen ruwa na ‘yankasuwa ta mashigar ruwan Hormuz.
Amurka ta kai hari kan wurare a Iran, wadda ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan kayayyakin Amurka a faɗin yankin.

















