Ministan Ilimi na Nijeriya, Tunji Alausa, ya umarci shugabannin jami’o’i da kwalejojin kimiyya da fasaha da na ilimi a faɗin ƙasar da su kori duk ɗalibin da aka samu da laifin shiga harkar garkuwa da mutane ko laifuka masu alaƙa da ita, bayan kammala bincike yadda ya kamata.
A cikin wata sanarwa da mai ba ministan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Ikharo Attah, ya sanya wa hannu, ya ce an umarci shugabannin manyan makarantu da su ƙarfafa tsarin tattara bayanan sirri na cikin gida tare da faɗaɗa haɗin gwiwa da Hukumar Tsaro ta DSS da sauran hukumomin tsaro a jihohinsu, a matsayin wani shiri na ƙasa baki ɗaya domin kare harabar makarantu da kuma tabbatar da tsaron ɗalibai.
Ministan ya bayar da wannan umarni ne yayin wata ganawa da shugaban majalisar gudanarwa, mambobin majalisar da kuma mahukuntan Jami’ar Tarayya ta Lafia da ke jihar Nasarawa, a ofishinsa da ke Abuja.
“Idan aka daɗe ana kyale munanan ɗabi’u, suna zama al’ada. Duk ɗalibin da aka samu, bayan cikakken bincike, da laifin shirya ko shiga satar ɗalibai takwarorinsa, ba shi da gurbi a manyan makarantunmu. Dole ne a kore irin waɗannan mutane. Bai kamata harabar makarantunmu ta zama mafakar masu aikata laifuka ba. Gwamnati na da alhakin kare rayukan marasa laifi da kuma tabbatar da cewa cibiyoyinmu sun ci gaba da kasancewa wuraren ilimi da nagarta,” in ji ministan.
Yayin da ya bayyana cewa jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi na Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai kyau ta fuskar tsaro, ministan ya ce wasu keɓaɓɓun abubuwan da suka faru kwanan nan da suka shafi ɗalibai a wajen harabar makarantu sun nuna akwai buƙatar ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro.
Ministan ya kuma bayyana cewa kwanan nan ya yi wata doguwar ganawa da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), domin samar da haɗaɗɗiyar dabarar ƙarfafa shirin Safe Schools Initiative da kuma inganta kariyar ɗalibai a faɗin ƙasar.
Alausa ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa samar da goyon bayan siyasa, jagoranci da albarkatun da ake buƙata domin inganta tsaron ƙasa tare da aiwatar da manyan sauye-sauye a fannin ilimi. A cewarsa, gwamnatin na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa kowane yaro ɗan Nijeriya ya samu ingantaccen ilimi a cikin muhalli mai aminci da dacewa.

















