Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana a ranar Alhamis cewa bai kamata ƙasashen Musulmai su bari a yi amfani da ƙasashensu wajen ƙaddamar da hare-hare kan sauran ƙasashen Musulmai ba.
“Kare Iran ba ya nufin gaba da sauran ƙasashen Musulmai ko kuma ƙasashe masu maƙwabtaka,” kamar yadda Pezeshkian ya bayyana a wani jawabin da ya yi a gidan talabijin na ƙasar yayin taron ƙasa da ƙasa na Haɗin kan Musulmai a Tehran.
“Bai kamata wata ƙasar Musulmai ta bari a yi amfani da ƙasarta ba wajen ƙaddamar da hari kan wata ƙasar Musulunci ba. babu wata ƙasar Musulunci da ya kamata ta nemi kariyarta ta hanyar rashin tsaron maƙwabtanta,” in ji shi.
Da yake magana game da yaƙi da Amurka, Pezeshkian ya ce manyan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran sun fara ne yayin da ake ƙoƙarin diflomasiyya tsakanin Tehran da Washington domin warware matsalolinsu.
Ya ce tattaunawar Iran da Amurka ta kankama a cikin wannan watan a ƙoƙarin neman mafita ta diflomasiyya a lokacin aka fara kai hare-haren, inda suka kashe kwamandojin Iran da jami’ai da masana kimiyya da ɗalibai da ƙananan yaran makarata da fararen hula tare da kai hari kan birane da ababen more rayuwa.
Kamfanin dillancin labaran IRNA da ƙasar Iran ke jagoranta ya ce kimanin baƙi na cikin gida da na ƙetare 600 daga ƙasashe 40 ciki har da Iraq da Pakistan da Turkiyya da Lebanon da Afghanistan ne ke halartar taron.
Taron zai ci gaba har zuwa ranar Lahadi inda za a yi zama a Tehran da Qom da Mashhad tare da tarukan na musamman a lardunan West Azerbaijan da Kordestan da Golestan da kuma Razavi Khorasan.

















