Wasanni

Sakon Lionel Messi na yin ritaya daga buga kwallo a matakin kasa-da-kasa

A ƙarshe ya kammala da cewa, “Ina bankwana cike da kwanciyar hankali da alfahari, kasancewar ni da abokan wasana, mun yi matuƙar ƙayatar da ku… Ina son ku duka. Na gode wa Allah da ya yi ni ɗan Argentina”.

Newstimehub

Newstimehub

31 Aug, 2026

922ae41b 1991 4859 b4a8 26a40cd2d3e4 1786197332563

Gwarzon ƙwallon ƙafa ɗan Argentina, Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa a matakin ƙasa-da-ƙasa, wanda ke nufin ba zai sake buga wa tawagar ƙasarsa Argentina wasa ba.

Messi ya sanar da ritayar ne a saƙonsa na Instagram a Litinin 31 ga Agustan 2026, inda ya ce, “Bayan duka wannan lokaci tun daga wasan ƙarshe [na FIFA 2026], sannan bayan yin nazari sosai, ina mai sanar da kowa cewa na yi ritaya daga tawagar ƙasata”.

“Mataki ne mai ciwo, kuma har yanzu yana min ciwo a rai, amma na fahimci cewa wannan ne lokacin da ya dace. Ina mai rantsuwa cewa na sadaukar da komai, ba kawai a ‘yan shekarun baya ba lokacin da muka lashe komai, amma har kafin nan ma. Na yi yaƙi da sadaukarwa don wannan jesin, don ba ku nishaɗi da alfaharin kasancewa ‘yan Argentina ta amfani da ƙwallon ƙafa.”

Messi ya kuma ƙara da cewa, “Na ba da komai da nake iyawa; Ba ni da wani ƙarin abin bayarwa, kuma akwai wasu haziƙan matasan ‘yanwasa da suka taso waɗanda ke buƙatar dama”.

“Na gode kan duka soyayyar da na gani cikin fiye da shekaru 20 ɗin nan. Zan yi kewar jin muryoyin goyon bayanku daga ciki da wajen filin wasa. Godiya ga iyalaina kan kasancewa tare da ni a wannan kyakkyawar tafiya mai wahala…. Na gode ga duka koci-koci, abokan wasa, da jami’ai da muka kasance tare a wannan tafiya.”

A ƙarshe ya kammala da cewa, “Ina bankwana cike da kwanciyar hankali da alfahari, kasancewar ni da abokan wasana, mun yi matuƙar ƙayatar da ku… Ina son ku duka. Na gode wa Allah da ya yi ni ɗan Argentina”.

Mutuwar mahaifi

Wannan na zuwa ne yayin da Messi ya gaza lashe Kofin Duniya tare da tawagar Argentina a gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 da aka kammala a watan Yuli, duk da sun je wasan ƙarshe. Argentina ce ta lashe kofin a 2022, inda Messi ya ci burin saka lashewa kafin yin ritaya.

Haka nan wannan matakin nasa ya zo ne makonni uku bayan rasuwar mahaifinsa, Jorge Messi, wanda ya mutu ranar 8 ga Agustan 2026 yana da shekaru 68.

A ta’aliƙin da ya rubuta a ƙarshen saƙon nasa na Instagram, Lionel Messi ya bayyana cewa tun ranar 21 ga Yuli ya rubuta wasiƙar ritayar a takarda, kwanaki biyu bayan wasan ƙarshe na Kofin Duniya. Sannan bayan abin da ya faru da mahaifinsa, ya samu cikakkaiyar gamsuwa kan matakin.

Messi dai shi ne ɗanwasan tawagar Argentina da ya fi kowa bugawa ƙasarsa wasa. Daga Agustan 2005 zuwa Agustan 2026 ya buga wasanni 207, ya ci ƙwallo 125 da tallafin ƙwallo 65, wanda ya sa ya zama ɗanwasan da ya fi kowa ciyo wa Argentina ƙwallo a tarihi.

Lionel Messi ya yi ritaya yana da shekaru 39 a duniya, kuma bayan bugawa ƙungiyoyin Barcelona ta Sifaniya da PSG ta Faransa, a yanzu yana ci gaba da buga wa ƙungiyar Inter Miami da ke Amurka.