Wani rahoton bincike da Majalisa Dinkin Duniya (MDD) ta fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa makamai na ƙasashen waje da fasahar soja da mayaka da kuma hanyoyin dabarun sadarwa suna taka rawa wajen ci gaban rikicin Sudan tare da faɗaɗa ikon ɓangarorin da ke yaƙi da juna wajen kai hare-hare kan yankunan fararen hula da jiragen sama marasa matuƙa.
Yaƙin Sudan, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin Sudan da Rundunar kai dauƙin Gaggawa ta (RSF), ya raba mutane fiye da miliyan 14 da muhallinsu kuma ya haifar da ɗaya daga cikin mawuyacin yanayin jinƙai a duniya, a cewar MDD
An kashe mutane fiye da 1,000 a hare-haren jiragen sama marasa matuƙa a cikin watanni biyar na farko na 2026, a cewar binciken rahoton da tawagar MDD ta fitar, inda ta zargi ɓangarorin biyu da aikata manyan laifuka na take haƙƙin ɗan adam da na ƙasa da ƙasa tare da wasu nau’ikan laifin da ake zargin za su iya zama laifukan yaƙi, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya bayyana.
Ko da yake rundunar RSF da sojojin Sudan ba su amsa buƙatun Reuters na tsokaci kan batun ba, amma a baya dukansu sun musanta zargen cin zarafi.
Yaƙi da jirage marasa matuƙa
Tawagar binciken ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce bincikenta kan tallafin da Sudan ke samu daga waje yana matakin farko, amma ta gano shaidar cewa akwai jiragen sama marasa matuka da ake amfani da su daga ƙasashen waje da kuma manyan makamai masu linzami – waɗanda za su iya shawagi a kan wani yanki kafin su kai hari – sun faɗaɗa ƙarfin sojojin na kai hari mai nisa.
Ta ce an yi amfani da wasu daga cikin waɗannan makaman wajen kai hare-hare a wuraren fararen hula, ciki har da Kasuwar Yabus a Jihar Blue Nile.
Faɗaɗa kewayon jiragen sama marasa matuka, juriya da kuma ƙarin ƙwarewa sun bai wa sojojin Sudan da RSF damar kai hare-hare masu nisa, kuma shaida ta nuna ɓangarorin biyu suna kai hare-haren jiragen sama marasa matuka waɗanda suka kashe fararen hula kuma suka kai hari kan asibitoci, makarantu, kasuwanni da wuraren da ‘yan gudun hijira ke zaune, in ji rahoton.
Tsakanin watan Mayu da Yuli na 2026, hare-haren jiragen sama marasa matuka na RSF sun lalata cibiyoyin wutar lantarki da wuraren mai a babban birnin Arewacin Kordofan na El Obeid, wanda ke ƙarƙashin ikon sojoji yayin da matsin lambar RSF ta ƙaru a watan Yunin wannan shekarar.
Hare-haren sun kawo cikas ga samar da ruwa, kiwon lafiya, sufuri da sauran ayyukan yau da kullun a cikin birnin da ke fuskantar matsin lamba da kuma killace wani bangare.
Daga cikin batutuwan da rahoton ya tabo akwai hare-haren sojoji da masu bincike suka ce sun kashe akalla mutane 70 a Asibitin Koyarwa na Ad-Da’ein da ke Gabashin Darfur.
Tawagar ta sake nanata kira da a aiwatar da takunkumin makamai a yankin Darfur tare da yin kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya tsawaita shi a duk fadin Sudan.

















