Wasanni

Masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafar Nijeriya na taron tattauna hanyoyin kawo gyara

Tattaunawar na zuwa ne bayan Nijeriya ta gaza samun damar shiga Gasar Kofin Duniya sau biyu a jere.

Newstimehub

Newstimehub

15 Sep, 2026

90c1f83c 716e 477e 8ddd 4581caea0cfa 1789476921684

Masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafar Nijeriya sun gabatar da shawarwari daban-daban na kawo gyara a harkar gudanarwa ta ƙwallon ƙafar ƙasar yayin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ke ci gaba da neman shawarwari a Abuja.

Shuwagabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi (FA) sun yi kira da a samar da sauyi ƙarƙashin jagoranci na cikin gida, yayin da wakilai na ‘yanwasa da koci-koci da lafiri-lafiri suke goyon bayan tsarin daidaita lamurra a ƙarƙashin jagorancin masu ruwa da tsaki.

An fara tattaunawar ne ranar Litinin biyo bayan ajiye aikin tsohon shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) Ibrahim Gusau kuma ana tsammannin za ta ci gaba ranar Talata, inda FIFA da CAF suka shirya nazari kan shawarwarin da ƙungiyoyin daban-daban suka gabatar kafin su ba da shawara game da mataki na gaba.

Yakubu Sarma, shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta jihar Gombe kuma shugaban tawagar shuwagabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi, ya ce hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi suna goyon bayan gyare-gyare amma sun yi imanin cewa ya kamata a aiwatar da su ta hanyar tsare-tsaren da ke akwai a cikin Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF).

Shawarwarin sauyin da aka gabatar

“Muhimmin batu da muka gabatar ga FIFA a matsayin mambobin tawagar da ke wakiltar hukumomin ƙwallon ƙafa na jihohi shi ne harkar ƙwallon ƙafar Nijeriya ba ta cikin wani rikici domin gasar lig ɗinmu na tafiya ƙungiyoyin ƙwallon ƙafarmu na wasa a matakin nahiya ‘yanmatanmu na wasan ƙasa da ƙasa kuma sakatariyar NFF na aiki,” kamar yadda Sarma ya shaida wa ‘yanjarida bayan ganawa da tawagar FIFA.

Sarma ya ce Hukumomin Ƙwallon ƙafa na jihohi ba su yi adawa da gyara ba, yana mai cewa yawancin sauye-sauyen da aka ba da shawarar yi an riga an saka su a cikin sauye-sauyen dokokin NFF.

Wakilan ‘yanwasa da koci-koci da lafiri-lafiri, kuwa sun yi kira da a faɗaɗa yawan masu taka rawa a harkar tattaunawar.

Ana tsammanin FIFA da CAF za su yi nazari a kan shawarwarin kafin su yanke hukunci a kan mataki na gaba na aikin gyaran.

Tattaunawar na zuwa ne bayan Nijeriya ta gaza samun damar shiga Gasar Kofin Duniya sau biyu a jere da kuma matsi da Hukumar Wasanni ta Nijeriya ke yi domin samar da sauyi wajen gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa na ƙasar.