Al’umma jihar Neja da ke yankin Arewa maso tsakiyar Nijeriya sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin 22 ga Satumba don kira ga gwamnati kan daruruwan mutanen da suka ce suna hannun ‘yanbindiga wata ɗaya bayan da aka yi garkuwa da su.
Harin da ‘yanbindigar suka kai kan al’ummomi da dama a Jihar na ɗaya daga cikin manyan satar mutane da aka taba yi a Nijeriya.
Masu zanga-zangar, daga ƙauyen Dekara da al’ummomin da ke makwabtaka da su a karamar hukumar Borgu inda suka ce ‘yanbindiga sun sace mutane kusan 600, wadanda galibinsu mata da yara da kuma tsofaffi ne, sun taru a hedikwatar gwamnatin yankin da ke New Bussa don neman a saki waɗanda aka yi garkuwa da su.
Borgu na da nisan kilomita 300 (mil 186) daga babban birnin jihar Minna, kana daga Yamma yana kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Benin.
Zanga-zangar ta ƙara matsin lamba ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu don magance matsalar rashin tsaro a ƙasar, lamarin da zama babban batu da ya fi mayar da hankali gabanin babban zaɓen Nijeriya a Janairun 2027.
Ko da yake Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a yi gaggawar ceto mutanen da aka sace bayan hare-haren na ranar 21 ga Agusta, sai dai har yanzu ba a kai ga gano su ba. “An tura hukumomin tsaro, amma har yanzu ba mu samu amsa daga gare su ba.
Gwamnati tana ƙoƙarin ceto mutanen,” kamar yadda Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Neja Obed Nuhu Nana ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters.
‘Kusan mutane 700 aka yi a garkuwa da su’
Mazauna yankin sun bayyana cewa, ‘yanbinduga sun yi garkuwa da mutane fiya da 600, adadin da hukumomi ba su tabbatar ba kawo yanzu.
Abdullahi Yahaya Sadauki, shugaban ƙungiyar ci gaban matasa ta Karamar Hukumar Borgu, ya ce al’ummomi yankin sun kiyasta cewa kusan mutane 700 ne suke hannun masu garkuwa da mutane.
“A yi ƙidayar a ƙauyuka. Wannan ita ce hanya mafi kyau da za ta tabbatar ko ikirarinmu gaskiya ne ko a’a,” in ji Sadauki.
Ko da yake kafar Reuters ba ta iya tabbatar da adadin ba da kanta.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar kana memba a ƙungiyar mai suna Abdulmalib Dindey, ya ce rashin tsaro ya takaita zuwan mazauna yanki kasuwanni da duba lafiyarsu.
Hanifa Konkoso, mai shekaru 26, ta ce an rufe shaguna a Borgu duk da cewa ranar Litinin ce ranar kasuwa.
“Muna son gwamnati ta dauki mataki,” in ji ta, inda ta kara da cewa mazauna yankin na ci gaba da matsa wa hukumomi lamba don tabbatar da sakin wadanda aka kama da kuma dawo da tsaro.

















