Jami’an NDLEA sun gano tare da hana wasu yunƙurin safarar miyagun ƙwayoyi ta hanyoyi da ba a saba gani ba. Hukumar ta ce an kama mutane uku, ciki har da wata mata da ta yi amfani da cikin bogi domin ɓoye Tramadol, da kuma wani da ya haɗiye hodar Iblis.
A kan iyakar Seme Border, jami’ai sun kama Rabi Muhammad, ‘yar kasuwa mai shekara 35 daga Kano, yayin yunƙurinta na shiga Cotonou. Bayan bincike, an gano ta ɓoye kafso 3,200 na Tramadol a cikin wata ƙwarya da ta daure a cikinta domin kwaikwayon juna biyu.
A Malam Aminu Kano International Airport kuma, jami’an NDLEA sun kama Michael Gohouri, ɗan Ivory Coast mai shekara 41, yayin shirin tafiya Milan ta Addis Ababa. Gwajin na’ura ya nuna ya haɗiye miyagun ƙwayoyi, inda daga bisani ya fitar da kunshe 82 na hodar Iblis masu nauyin kilo 1.49.
Hukumar ta ce wanda ake zargin ya yi zirga-zirga tsakanin Legas, Enugu da Kano kafin ya haɗiye ƙwayoyin, tare da alƙawarin samun Euro 5,000 idan ya kai kayan zuwa Italiya. NDLEA ta jaddada aniyar ta na ci gaba da daƙile sabbin dabarun safarar miyagun ƙwayoyi.














