Hauhawar farashi a Najeriya ta ragu zuwa kashi 15.15 cikin 100 a watan Disambar 2025, abin da ke nuna rage matsin farashi da alamun daidaituwar tattalin arziki a ƙarshen shekara, a cewar Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS).
Bayanan da NBS ta fitar a ranar Alhamis sun nuna cewa CPI ya tashi zuwa 131.2 a Disamba daga 130.5 a Nuwamba, amma saurin tashin farashin ya ragu. A ma’aunin wata-zuwa-wata, hauhawar farashi ta sauka zuwa 0.54% daga 1.22% a watan Nuwamba.
A shekara-zuwa-shekara, hauhawar farashi ta ragu daga 17.33% a Nuwamba, kuma ta yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da 34.80% da aka samu a Disambar 2024, bisa sabon tsarin base year na Nuwamba 2009.
NBS ta danganta raguwar da aka samu da sabunta tsarin CPI, wanda aka ce gyaran fasaha ne domin ya fi dacewa da halin tattalin arziki na yanzu, tare da jaddada cewa hakan ba alamar tabarbarewar tattalin arziki ba ce.
A birane, hauhawar farashi ta ragu zuwa 14.85% a shekara-zuwa-shekara daga 37.29% a Disambar 2024, yayin da na wata-zuwa-wata ya ɗan tashi zuwa 0.99%. Matsakaicin watanni 12 a birane ya tsaya a 23.46%.
A yankunan karkara kuwa, hauhawar farashi ta sauka zuwa 14.56% a shekara-zuwa-shekara daga 32.47% a shekarar da ta gabata, tare da ragin wata-zuwa-wata na 0.55%. Matsakaicin watanni 12 a karkara ya kai 21.93%.













