Nijeriya

‘Yansandan Nijeriya sun ceto mutane 10 daga cikin ‘yan NYSC da aka yi garkuwa da su a jihar Imo

Mai magana da yawun rundunar, Henry Okoye, ya shaida wa kafar yada labarai ta Channels Television cewa, an gudanar da aikin ceto ne bayan da wasu gungun ’yanbindiga suka kai hari kan wasu motocin bas biyu da ke ɗauke da ’yan NYSC da wasu fasinjoji.

Newstimehub

Newstimehub

2 Oct, 2026

11d89972 cedf 4311 a4e4 eae64102d782 1789459860322

Rundunar ’yansandan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Nijeriya ta ce jami’anta sun ceto mutane 10 daga hannun ’yanbindiga da suka yi garkuwa da su a kan hanyar Owerri zuwa Onitsha.

Mai magana da yawun rundunar, Henry Okoye, ya shaida wa kafar yada labarai ta Channels Television cewa, an gudanar da aikin ceto ne bayan da wasu gungun ’yanbindiga suka kai hari kan wasu motocin bas biyu da ke ɗauke da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da wasu fasinjoji.

A cewar rundunar, harin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, kusa da Umunoha.

Motocin na kan hanyarsu ne daga garin Ibadan na jihar Oyo zuwa Uyo a jihar Akwa Ibom da kuma Bende na jihar Abia, lokacin da ’yanbindigar suka tare su.

Rundunar ta ce tana ci gaba da tantance ainihin adadin mutanen da aka sace, yayin da jami’an tsaro ke gudanar da bincike tare da bin sahun masu garkuwar domin ceto sauran waɗanda ake tsare da su.

Kwamishinan ’yansandan jihar, Audu Bosso, tare da kwamandojin sauran hukumomin tsaro, sun ziyarci wurin da lamarin ya faru domin duba halin da ake ciki da kuma tsara matakan ceto.

’Yansandan sun ce za su ci gaba da aikin har sai an ceto dukkan waɗanda aka sace tare da cafke waɗanda suka aikata laifin.

An sake buɗe ɓangaren hanyar Owerri zuwa Onitsha da lamarin ya shafa, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kasancewa a yankin domin kare masu amfani da hanyar.

Rundunar ta ce tana aiki tare da hukumar NYSC wajen tuntubar iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma sanar da su halin da ake ciki.

Ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin nutsuwa da taka-tsantsan, tare da bayar da bayanan da za su taimaka wajen ceto sauran waɗanda aka sace.

Lamarin ya faru ne makonni kaɗan bayan da jami’an tsaro suka ceto masu yi ƙasa hidima na NYSC 15 da wasu mutane shida da aka sace a jihar Kogi.

Daga baya an kubutar da su bayan wani samame da jami’an tsaro suka gudanar bisa bayanan sirri a dajin Egume, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafke masu garkuwar.