Gwamnatin ƙasar Gabon ta sanar da dakatar da tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa bayan abin da ta bayyana a matsayin mummunan aiki da ya zubar da mutunci a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON 2025 da ake gudanarwa a Morocco.
Ministan Wasanni na ƙasar ya bayyana matakin a kafar talabijin bayan Gabon ta ƙare wasannin rukuni a matsayi na ƙarshe, inda ta sha kashi a wasanni uku tare da ficewa daga gasar tun a matakin rukuni.
Mukaddashin Ministan Wasanni, Simplice-Desire Mamboula, ya ce bayan rashin nasarar da Gabon ta yi da ci 3-2 a hannun Ivory Coast a Marrakech, gwamnati ta yanke shawarar rushe tawagar masu horaswa, dakatar da tawagar ƙasa har sai abin da hali ya yi, da kuma cire ‘yan wasa Bruno Ecuele Manga da Pierre-Emerick Aubameyang daga tawagar.
Gabon, ƙarƙashin jagorancin tsohon ɗan baya Thierry Mouyouma, ta riga ta fita daga gasar bayan shan kaye a hannun Cameroon da Mozambique a wasannin farko na Rukuni F. Duk da sun fara wasa na ƙarshe da Ivory Coast da kwallaye biyu babu ko ɗaya, sun bari aka rama musu da kwallaye uku daga tawagar da ba cikakkiya ba ta Ivory Coast.
Dangane da Aubameyang, tsohon gwarzon ƙwallon ƙafar Afirka, bai buga wasan na ƙarshe ba sakamakon raunin cinyarsa, lamarin da ya sa ya koma kulob ɗinsa na Faransa, Olympique de Marseille, domin jinya.
A martaninsa a kafar sada zumunta ta X, Aubameyang ya ce: “Ina ganin matsalolin tawagar sun fi mutum ɗaya girma.”
Aubameyang mai shekaru 36, da kuma tsohon ɗan bayan Cardiff City Bruno Ecuele Manga mai shekaru 37, na iya kasancewa sun buga wasanninsu na ƙarshe ne da tawagar Gabon.
Masana sun nuna cewa irin wannan mataki na rushe tawagar ƙasa ya kasance ruwan dare a baya, sai dai a yanzu ya zama abu mai wuya tun bayan da FIFA ta fara ɗaukar tsauraran matakai kan tsoma bakin gwamnati a harkokin ƙwallon ƙafa na ƙasashe.














