An shiga sabon babi mai cike da armashi a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta CAF AFCON Morocco 2025, yayin da aka kammala wasannin rukuni cikin gasa mai zafi da ta nuna ƙarfin ƙwallon ƙafa a faɗin Afirka. Yanzu haka, hankali ya koma zagayen 16, inda kowace ƙungiya ke fafutukar kaiwa matakin kwata-final.
Wasannin zagayen 16 za su gudana daga Asabar 3 Janairu zuwa Talata 6 Janairu, inda za a buga wasanni biyu a kowace rana. Lokutan tashi wasa su ne 17:00 na yamma (16:00 GMT) da kuma 20:00 na dare (19:00 GMT).
Zagayen zai buɗe ne da wasan Senegal, zakarun 2021, da Sudan a filin wasa na Grand Stade de Tanger da yammacin Asabar. Daga bisani kuma, Mali za ta fafata da Tunisia a Stade Mohammed V da ke Casablanca, inda Mali ke neman kambu na farko, yayin da Tunisia ke son tunawa da nasararta ta 2004.
A ranar Lahadi, masu masaukin baki Morocco za su kara da Tanzania a Stade Prince Moulay Abdellah da ke Rabat. Morocco na da burin lashe AFCON na farko cikin shekaru 50, bayan sun yi fintinkau a Rukuni A, yayin da Tanzania ta tsallaka ne a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙungiyoyin matsayi na uku.
Daga baya a wannan rana, Afirka ta Kudu za ta kara da Kamaru, a wasan da zai sake haɗa koci Hugo Broos da tsohuwar ƙungiyarsa da ya jagoranta zuwa nasarar AFCON a 2017.
A ranar Litinin, ƙasar da ta fi lashe AFCON sau bakwai, Masar, za ta fafata da Benin a Grand Stade d’Agadir. Fir’aunonin Masar na fatan kawo ƙarshen jiran kofin da ya kai tun daga 2010. Haka kuma a wannan rana, Najeriya za ta kara da Mozambique a Complexe Sportif de Fès, inda Super Eagles ke neman zarcewa fiye da matsayi na biyu da suka samu a AFCON 2023.
Zagayen zai ƙare a ranar Talata da wasan Aljeriya da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo), kafin daga bisani Ivory Coast, masu kare kambu, su kara da Burkina Faso a Grand Stade de Marrakech.
An tsara buga wasannin kwata-final a ranakun 9 da 10 Janairu, yayin da wasan ƙarshe zai gudana a ranar 18 Janairu a Stade Prince Moulay Abdellah da ke Rabat.














