Hukumar Kula da Wasanni ta Ƙasa (NSC) ta yi bayani kan dalilin jinkirin biyan ladan ’yan wasan Super Eagles a gasar AFCON 2025, bayan da ƙungiyar ta yi barazanar kaurace wa wasan daf da karshe da Algeria.
Shugaban NSC, Shehu Dikko, ya ce jinkirin ya samo asali ne daga matsalolin tsarin gwamnati, yana mai tabbatar da cewa an riga an amince da kuɗin kuma ana kan aiwatar da su. Ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar Channels Television a ranar Alhamis.
Dikko ya ce dukkanin hukumomi da suka haɗa da NFF, NSC, Fadar Shugaban Ƙasa, Ma’aikatar Kuɗi da Babban Bankin Nijeriya (CBN) na da hannu a tsarin fitar da kuɗin. Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da kasafin kuɗin AFCON tun a ranar 14 ga Nuwamba, amma fitar da kuɗin na buƙatar lokaci.












