Patrice Motsepe shugaban hukumar kula da harkokin ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), , ya bayyana a ranar Asabar cewa daga shekarar 2028 za a riƙa gudanar da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON) duk bayan shekara huɗu-huɗu.
Motsepe ya ce wannan mataki na daga cikin manyan sauye-sauyen da CAF ke shirin kawowa a harkar ƙwallon ƙafar Afirka, domin a daidaita jadawalin gasar da tsarin ƙwallon ƙafa na duniya. Ya bayyana cewa duk da cewa shirya gasar AFCON bayan shekaru biyu-biyu na samar wa ƙungiyoyin Afirka kuɗin shiga, CAF na da burin ƙaddamar da gasar lig ta ƙasashen Afirka, wadda za ta yi kama da gasar UEFA, domin ƙara wa ƙasashen kudaden shiga.
“Babban abin da ke gabanmu a yanzu shi ne gasar AFCON, amma daga shekarar 2027 za mu je Tanzania, Kenya da Uganda, sannan gasar AFCON ta gaba ita ce wadda za a gudanar a 2028,” in ji Motsepe yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Rabat na ƙasar Maroko, a daidai lokacin da ake shirin soma AFCON 2025.
Damar ɗaukar nauyin gasar
Motsepe ya kuma bayyana cewa CAF za ta bai wa ƙasashen da ke sha’awa damar neman ɗaukar baƙuncin Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka ta 2028. “Bayan Gasar Cin Kofin Duniya ta Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafa ta FIFA a 2029, za mu ƙaddamar da gasar lig ta ƙasashen Afirka ta farko, inda za a zuba ƙarin kuɗaɗe, kayan aiki da gasa mai ƙarfi. “A matsayin wani ɓangare na wannan tsari, za a riƙa gudanar da gasar AFCON duk bayan shekara huɗu-huɗu,” in ji shi.














