Afirka ta Kudu ta buƙaci ƙasashen Afirka da ta mayar da jama’arsu gida su biya ta ladan jigila

Afirka ta Kudu na buƙatar gwamnatocin sauran ƙasashen Afirka da dama su biya ta kuɗaɗen da ta kashe wajen jigilar dubban ‘yan ƙasashensu zuwa gida.
12 Aug, 2026
Sojojin Sudan sun dakile hare-haren jiragen yaki maras matuka na RSF a Khartoum da Kogin Nilu

Hare-haren jiragen sama marasa matuƙa na RSF na baya-bayan nan sun mayar da hankali kan wuraren soji da muhimman kayayyakin more rayuwa a biranen da sojoji ke rike da ikonsu a Sudan.
12 Aug, 2026
Yankuna uku na Ghana za su fuskanci katsewar wutar lantarki, in ji kamfanin ECG

Katsewar wutar na daga wani ɓangare na ayyukan gyara da kamfanin ya tsara da nufin ƙara ingancin wutar lantarki.
12 Aug, 2026
Fiye da mutum 5000 sun tsere saboda rashin tsaro da ke daɗa ƙamari a Darfur ta Yamma a Sudan: MDD

Da yawa daga cikin iyalan da lamarin ya shafa sun kasance waɗanda aka tilasta musu barin gidajensu ne kuma suka ƙetare zuwa cikin, in ji hukumar IOM ta Majalisar Dinkin Duniya.
10 Aug, 2026

Hatsarin mota ya kashe mutum 22, ciki har da sojoji 17 a Nijar

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta yi kira ga Chadi ta janye matakinta na ficewa daga kotun

Guinea ta nemi Faransa ta mayar da ƙoƙon kawunan ‘yan ƙasarta masu fafutuka

Kenya na binciken abin da ake tunanin guba ce wadda ta kashe giwaye 16

Kwamitin tattaunawa na Libiya ya cim ma matsaya kan tsarin ɗaukar shugaban hukumar zaɓe
4 Aug, 2026
Shugaba Biya na Kamaru, wanda ba ya nan, ya yi sauye-suaye a shugabancin sojin ƙasar
An sanya hannu a kan dokokin ne a ranar Litinin kuma an sanar da matakin ta gidan radiyon kasa.

3 Aug, 2026
Ghana ta amince da ɗaurin shekara 20 ga duk wanda ya mayar da gonar koko zuwa wani abu daban
Hukumomi sun ce dokar za ta bai wa dukkan gonakin koko kariya, lamarin da zai mayar da yin wani abu daban da gonakin koko laifi.

3 Aug, 2026
Ɗaruruwan mutane sun yi hijira daga kudu maso yammacin Nijar saboda hare-haren ‘yanta’adda
Wasu daga cikin mutanen da suka tsira sun tsere zuwa yankin Tahoua da ke kusa da iyakar Nijeriya, yayin da wasu ɗaruruwa suka nemi mafaka a Dogondoutchi, wani babban gari da ke da nisan kusan kilomita 100.

1 Aug, 2026
‘Yan Boko Haram sun kashe sojojin Nijar, in ji kafar watsa labaran gwamnati
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Jamhuriyar Nijar ANP bai faɗi adadin sojojin da aka kashe ba, sai dai ya tabbatar da cewa an kashe sojoji a harin da aka kai a kusa da garin N’Guigmi da ke yankin Tafkin Chadi.

31 Jul, 2026
Adadin ‘yan ci-ranin da suka rasu ya kai 19 bayan dubbai sun tsallaka zuwa yankin Ceuta na Sifaniya
Sifaniya ta tura dakaru tare da rufe kan iyakarta a Melilla bayan an samu isowar mutane da yawa daga Maroko, yayin da Rabat ke ƙoƙarin hana ƙarin tsallakewar mutane.

31 Jul, 2026
Gwamnatin Ghana ta amince da shawara ƙara wa’adin mulkin shugaban ƙasa
Shawarar na daga wani ɓangare na shirin gyaran kundin tsarin mulkin Ghana.

30 Jul, 2026
Biranen Afirka 25 da Amurka za ta rufe ayyukan bayar da biza daga ranar 1 ga Agustan 2026
A tsakiyar watan Yulin 2026, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da dakatar da bayar da biza daga birane 25 a faɗin Afirka, inda tilas masu neman bizar su tafi wasu biranen a abin da Washington ta bayyana “cibiyoyin yanki.”

28 Jul, 2026
Nijar ta dakatar da kamfanonin dillancin siminti 36 kan zargin ɓoye shi don haddasa ƙarancinsa
Gwamnatin ta Nijar ta zargi dillalan da boye siminti mai yawa duk da shirin gwamnati na sayar da siminti a farashi mai rangwame domin sauƙaƙa wa jama’a samun kayan gini.

28 Jul, 2026
Hukumomin Libya a Benghazi sun kori baƙin-haure fiye da 117,000 daga ƙasar
Akwai ‘yan Sudan fiye da 100,000 waɗanda suka amince su koma ƙasarsu bisa raɗin kansu yayin da hukumomin na Libya suka fitar da baƙin-haure 117,350 aƙalla daga ƙasar.

27 Jul, 2026
Mutumin da ya fi kowa tsawo a Ghana Awuche ya rasu
Sulemana Abdul Samed, wanda ake ganin shi ne namijin da ya fi kowa tsawo a Ghana, ya rasu yana da shekara 32, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar(GBC), ta ruwaito ranar Litinin.



