Nijeriya

An kashe ɗalibai yayin da sojoji suka ‘ceto ɗalibai 46’ daga harin satan ɗalibai a Borno

Babu tabbacin ko ɗalibai da suka rasun ‘yan makarantar FGGC Monguno ne ko kuma ‘yan Kolejin Kimiyya da Fasahar.

Newstimehub

Newstimehub

19 Jul, 2026

c7b8fc6a ae29 4238 a77a 7567b067b572 1784469999132

Dakarun Operation Hadin Kai da ‘yansandan Nijeriya sun daƙile wani ƙoƙarin sace ɗalibai na ‘yata’addan Daesh a makarantar sakandare na ‘yanmata na Gwamnatin Tarayya (FGGC) a Monguno, jihar Borno.

Mohammed Goni, muƙaddashin jami’in watsa labaran rundunar Operation Hadin Kai, ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ranar Lahadi, yana mai cewa sojojin sun ceto ɗalibai 46 a makarantar.

‘Yanta’addan sun far ma makarantar ne da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar dare ranar Asabar bayan sun samu sun shiga wurin da taimakon wasu da suka haɗa baki da su, in ji sanarwar da keftin Mohammed Goni ya fitar.

Goni ya ce ɗalibai daga Kolejin Kimiyya da Fasa na Tarayya da ke Monguno ne ke amfani na wucen gadi da makarantar FGGC ɗin a lokacin da ‘yanta’addan suka kai harin.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ɗaliban sun mutu a lokacin da harsashai na ‘yanta’addan da ke tserewa suka same su yayin musayar wuta.

Babu tabbacin ko ɗalibai da suka rasun ‘yan makarantar FGGC Monguno ne ko kuma ‘yan Kolejin Kimiyya da Fasahar.

Sanarwar ta ce dakarun soji sun yi arangama da ‘yanta’addan inda suka nuna musu fin ƙarfi lamarin da ya hana su ci gaba da aika-aikarsu.

Kazalika sanarwar ta ce babu ɗalibin da ‘yanta’addan suka sace.