An saka sunan Turkiyya cikin jerin sunayen ƙasashen da ake zuwa yawon buɗe ido da suka fi kare muhalli a fitowa ta shekarar 2025 ta mujallar Wanderlust da miliyoyin mutane ke karantawa.
Mujallar Wanderlust wadda ɗaya ce daga cikin mujallun da suka fi daɗewa kuma aka fi martabawa kuma masoya tafiye-tafiye da ƙwararru a harkar yawon buɗe ido ke binta sawu da ƙafa, ana ganinta a matsayin muhimmiyar mai faɗa-a-ji kan ƙasashen da suka fi mayar da hankali kan kare muhalli.
Yadda mujallar, wadda ake karantawa da yawa a Turai da nahiyar Amurka da Oceania da kuma Asiya, ta fitar da sunan Turkiyya ya nuna yadda tsarin yawon buɗe ido mai kula da muhalli na ƙasar ke jan hankalin duniya.
A cikin maƙalar da ta yi a kan Turkiyya, mujallar ta bayyana kasancewar ƙasar a kan gaba a harkar yawon buɗe ido mai ɗorewa, inda ta yi nuni da Dutsen Nemrut – wani muhimmin wajen tarihi na Hukumar Ilimi da Fasaha da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) – a matsayin wani wuri da ya fita daban.
Da manyan manyan gumakansa, Nemrut ba wuri ne kawai da ke da muhimmancin al’ada ba kawai, amma ya zama wata muhimmiyar alama ta tsarin gudanarwa ta kare muhalli na Turkiyya, da ta samu damar shiga shafi ɗaya a Mujallar.
Rubutun mujallar ya kuma yaba wa ƙoƙarin da ƙasar ke yi na kiyaye muhimman wuraren tarihi 21 na hukumar ta UNECSO ta hanyar ayyuka masu ɗorewa.
Saka Turkiyya cikin mujallar Wanderlust ya nuna matsayinta a fannin al’adu da kuma yadda duniya ke iya ganin manufofinta na sanin ya kamata da kuma kare muhalli.
A cewar wata sanarwar da Ma’aikatar Al’adu da yawon buɗe ido ta fitar, Turkiyya ta jaddada kasancewarta a kan gaba ta duniya a harkar yawon buɗe ido mai ɗorewa ta hanyar matakai masu ƙarfi da kuma shirye-shirye masu tasiri a duniya.
A matsayin ɗaya daga cikin mujallu da suka fi tasiri a harkar tafiye-tafiye, Wanderlust na taimaka wa miliyoyin matafiya da suka fi bai wa muhalli fifiko damar zaɓi ta jerin sunayen ƙasashen zuwa da ke kare muhalli wanda take fitarwa a ko wace shekara.