Nijeriya

An warware rikici tsakanin Nijeriya da Burkina Faso kan jirgin saman Nijeriya da aka tsare — Tuggar

Tattaunawar da aka yi game da batun ranar Laraba an yi ta ne tsakanin jami’an Nijeriya da Burkina Faso a babban birnin ƙasar Ouagadougou.

Newstimehub

Newstimehub

18 Dec, 2025

7b8ba92d6c8b8d37ce3f14bc74a4a52d966ef091dd6e1c94d9eb58c67c67f9a1

Mai magana da yawun ministan ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa sojojin Nijeriyar da aka riƙe da su a Burkina Faso za su iya barin ƙasar nan ba da jimawa ba.

An warware rikicin da ya ɓarke tsakanin Nijeriya da Burkina Faso bayan jirgin saman dakon kaya na sojin saman Nijeriya ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso sakamakon matsalar na’ura, in ji ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Tuggar, Alkasim Abdulkadir, ya fitar ranar Laraba ta ce ɓangarorin biyu sun warware batun ne cikin lumana bayan ministan harkokin wajen Nijeriya ya gana da shugaban ƙasar Burkina Faso Ibrahim Traore.

An kama sojojin ne kusan makonni biyu da suka wuce bayan ƙungiyar ƙasashen Sahel (AES) ta bayyana saukar jirgin a matsayin wani mataki “da ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa”.

Amma rundunar sojin saman Nijeriya ta ce jami’an da ke tuƙin jirgin sun lura da wata matsalar na’ura ne lamarin da ya sa suka yi saukar gaggawa a Bobo-Dioulasso, wani gari a Burkina Faso, mafi kusa mai filin jirgin sama.

NAF ta ce saukar an yi ta ne bisa matakan tsaro da kuma tsare-tsaren harkar jiragen sama na ƙasa da ƙasa.

A makon da ya gabata dai wasu rahotannin da ba a tabbatar ba da sun ce Burkina Faso ta saki sojojin na Nijeriya 11.

Sai dai ministan harkokin wajen Nijeriyar ta bayyana cewa ba a saki sojojin ba tukunna, yana mai ƙarawa da cewa ana ƙoƙarin warware taƙaddamar nan ba da jimawa ba.

Tattaunawar da aka yi game da batun ranar Laraba an yi ta ne tsakanin jami’an Nijeriya da Burkina Faso a babban birnin ƙasar Ouagadougou.

Abdulkadir ya bayya cewa Tuggar ya miƙa saƙon haɗin kai da ‘yan’uwantaka daga Tinubu zuwa Traoré, yayin da ɓangarorin biyu suka bayyana hanyoyin da za su zurfafa dangantaka tsakaninsu.

Abdulkadir ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan inganta haɗin kai a fannin siyasa da tsaro da tattalin arziki.