Nijeriya

An yanke wa mutumin da ya ƙona mutane a masallaci a Kano hukuncin kisa ta hanyar rataya

A lokacin da aka gabatar da Abubakar a gaban kotu a ranar Litinin, Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyyaya ya same shi da duka laifuka huɗu da ake tuhumarsa da su.

Newstimehub

Newstimehub

26 May, 2025

gettyimages 184964298

Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin cinna wa masallata wuta a Masallacin ƙauyen Gadan a Ƙaramar Hukumar Geza a jihar.

Lamarin ya faru ne tun a ranar 15 ga Mayun 2024 inda mutumin ya ƙona masallatan a daidai lokacin da suke sallar asubahi.

Kusan mutum 11 ne suka rasu nan take sai kuma wasu mutum 12 suka rasa rayukansu a lokacin da ake kula da su a Asibitin Murtala da ke Kano.

A lokacin da aka gabatar da Abubakar a gaban kotu a ranar Litinin, Mai Shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyyaya ya same shi da duka laifuka huɗu da ake tuhumarsa da su, kamar yadda jaridar Daily Trust a Nijeriya ta ruwaito.

Laifukan da aka tuhume shi da su sun haɗa da kisa da yunƙurin aikata kisa, haifar da mummunar rauni da wasa da wuta, inda hakan ya saɓa wa sashe na 143,148 da 370 na kundin shari’a na Jihar Kano na shekarar 2000.