Nijeriya

Ana fargabar mutane 40 sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a jihar Jigawa a ke Nijeriya

Ana ci gaba da ayyukan bincike da ceto a Jihar Jigawa ta Njeriya bana kwale-kwale dauke da mata da yara ‘yan firamare ya kife a Karamar hukumar Ringim, inda ake fargabar rasa rayuka akalla 40.

Newstimehub

Newstimehub

20 Jul, 2026

086037f0 1e5d 40ea 8133 5abe9bc28ea8 1784549771637

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ta ce a kalla muane 40 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwalen.

‘Yan sanda sun ce an gano gangar jikin mutum guda, inda ake ci gaba da ayyukan neman sauran wadanda lamarin ya rutsa da su.

Masu kunna nutso na yankin, jami’an jinkai da ‘yan sa kai na bayar da gudunmawa a ayyukan.

Daraktan Tsare-Tsare na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina, Muhammad Bala Sanusi ya bayyana cewa ana ci gaba da ayyukan ceto kuma za a sanar da jama’a game da ayyukan.

An rawaito cewa wadanda hatsarin ya rutsa da su na dawo wa daga makaranta a lokaci da kwale-kwalen ya kife.

Har yanzu mahukunta ba su tabbatar da musabbabin hatsarin a, inda ake ci gaba da gudanar da bincike.

A wajen al’ummu da dama musamman a arewacin Nijeriya, amfani da jiragen ruwan kwale-kwale ne mafita wajen yin tafiye-tafiye a lokutan damina.

Amma yawaitar hatsarin jiragen ruwan na ci gaba da fito da irin hatsarin da ake da shi da ya shafi lodin d aya wuce ka’ida, rashin kayan tsaro da rashin riginan ninkaya.

Kwararrun tsaro su sha nanata kiran daukar tsauraran matakan sufurin ruwa d akuma zuba jari sosai don magance irin wannan ibtila’i.