‘Yan sandan Jihar Anambra sun samu nasarar ceto wani mutum da aka sace a yankin Isulo da ke Ƙaramar Hukumar Orumba South, yayin wani sintiri na yau da kullum da suka gudanar a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa mutumin, wanda ɗan asalin Obinagu–Isikweachi ne a Ƙaramar Hukumar Oji River ta Jihar Enugu, amma yana zaune a Afirka ta Kudu, an sace shi ne da yammacin ranar 1 ga Janairu, 2026, daga ƙauyensa.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce wasu ‘yan bindiga shida dauke da makamai, tare da rufe fuskokinsu da abin rufe fuska, ne suka yi garkuwa da mutumin.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro na haɗin gwiwa da ke ƙarƙashin Forward Operating Base, Aguata, sun ceto mutumin da safiyar ranar 15 ga Janairu, 2026, yayin da suke sintiri a yankin Isulo.
Mutumin ya bayyana cewa masu garkuwa da shi sun nemi kudin fansa har naira miliyan 40 daga matarsa da ‘yan uwansa. Sai dai ya samu damar tserewa daga maboyarsu, lamarin da ya kai ga ceto shi cikin nasara.
Bayan ceto shi, an yi masa tambayoyi kuma tuni aka haɗa shi da iyalansa. Rundunar ‘yan sandan ta ce tana ci gaba da amfani da bayanan sirri da mutumin ya bayar domin gano inda masu laifin suke da kuma cafke su.
Rundunar ta sake jaddada ƙudurinta na ci gaba da aikin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tana mai cewa za ta sanar da jama’a duk wani sabon ci gaba.














