Kasuwanci

Babban Bankin Ghana ya ba da sabbin sharruɗan kuɗaɗen ƙetare ga masu shiga da kayayyaki

An ɗauki wannan matakin ne domin a tabbatar da bin gaskiya da kuma halaccin cinikayya na ƙetare.

Newstimehub

Newstimehub

29 Aug, 2025

2025 07 25t090615z 1206431571 rc2ktfa6zwxp rtrmadp 3 ghana debt

Babban Bankin Ƙasar Ghana (BoG) ya fitar da sabon umarni wanda ke buƙatar masu shigar da kayayyaki da ke amfani da kuɗaɗen ƙetare su tabbatar cewa sun ba da bayanan da ake buƙata a rubuce, a wani ɓangare na matakan hana halatta kuɗin haram.

Umarnin, wanda Misis Aimee V. Quashie ta sanya wa hannu a madadin sakataren bankin, ya gyara ƙa’idojin shiga da fitar da kuɗaɗen ƙetare, kamar yadda kamfanin dillancin ƙasar Ghana ya rawaito.

Wani muhimmin ɓangare na gyaran ya mayar da hankali kan masu shigar da kayayyaki cikin ƙasar, waɗanda a yanzu ya zama dole su samar da wasu takardu domin amfani da kuɗaɗen ƙetare wajen ciniki a harkar kasuwancinsu.

Sanarwar ta BoG ta ce ana buƙatar masu shigar da kayayyaki ƙasar su gabatar da:” takardar shaidar ofishin kuɗin ƙetare da shaidar banki a matsayin hujjar cire kuɗin a banki ko kuma siyansa, da kuma takardar shiga da kaya da aka sanya wa hannu da rasiti da kuma kwantiragi.”