Ma’aikatar lafiya ta Sudan ta sanar a ranar Talata cewa an samu karuwar cutar kwalara a cikin kasar da ke fama da rikici, inda aka samu mutum 2,700 da suka kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 172 a cikin mako guda.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce kashi 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga jihar Khartoum, inda aka samu matsalar ruwan sha da wutar lantarki saboda hare-haren jiragen sama marasa matuka da aka dora laifin yin su a kan dakarun RSF (Rapid Support Forces), wadanda ke fada da sojojin kasar tun watan Afrilu na shekarar 2023.
An kuma samu rahoton barkewar cutar a kudancin kasar, tsakiyar kasar, da kuma arewacin kasar.
Kwalara cuta ce da ta zama ruwan dare a Sudan, amma barkewar cutar ta kara tsananta tun bayan barkewar yakin, wanda ya lalata tsarin ruwa, tsaftar muhalli, da kuma cibiyoyin kiwon lafiya da dama.
Ruwa mara tsafta
A makon da ya gabata, ma’aikatar ta ce mutum 51 sun mutu sakamakon kwalara daga cikin fiye da mutum 2,300 da aka samu rahoton sun kamu da cutar a cikin makonni uku da suka gabata, kashi 90 cikin 100 daga cikinsu a jihar Khartoum.
RSF a wannan watan sun kai hare-haren jiragen sama a fadin Khartoum, ciki har da tasoshin wutar lantarki guda uku, kafin a kore su daga wuraren da suka rage suna rike da su a babban birnin a makon da ya gabata.
Hare-haren sun lalata wutar lantarki, wanda ya shafi tsarin ruwan sha na yankin, kamar yadda kungiyar likitoci marasa iyaka (MSF) ta bayyana, wanda hakan ya tilasta wa mazauna yankin amfani da ruwan da ba tsafta.
“Tasoshin tace ruwa ba su da wutar lantarki kuma ba za su iya samar da tsaftataccen ruwa daga Kogin Nilu ba,” in ji Slaymen Ammar, mai kula da harkokin lafiya na MSF a Khartoum, a cikin wata sanarwa.
Kwalara, wata cuta mai sa gudawa da ke faruwa sakamakon shan ruwa ko abinci da ya gurbata, na iya kashe mutum cikin sa’o’i idan ba a yi magani ba.
‘Matsanancin hali’
Duk da haka, cutar na da saukin kariya da kuma magani idan ana samun tsaftataccen ruwa, tsaftar muhalli, da kuma kulawar lafiyar da ta dace.
Tsarin kiwon lafiya na Sudan, wanda tun farko ya kasance mai rauni, ya kai ga “matsanancin hali” saboda yakin, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.
Har zuwa kashi 90 cikin 100 na asibitocin kasar a wani lokaci sun kasance sun rufe saboda rikicin, kamar yadda kungiyar likitoci ta bayyana, inda ake yawan kai wa cibiyoyin lafiya hari da kuma kwashe kayayyakinsu.
Yakin, wanda yanzu ya shiga shekara ta uku, ya kashe dubban mutane, ya raba mutane miliyan 13 da muhallansu, kuma ya haifar da babbar matsalar gudun hijira da yunwa a duniya.