Gwamnatin Burundi tare da Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijira (HCR) sun amince da wani babban shiri na dawo da sama da ‘yan gudun hijira 100,000 daga Tanzania da sauran kasashen da suka ba su mafaka. Ministan harkokin cikin gida, Léonidas Ndaruzaniye, ya bayyana cewa kudin shirin ya haura dala miliyan 82, kuma ana sa ran kammala mayar da wadanda ke Tanzania zuwa watan Yuni 2026, tare da rufe sansanonin Nduta da Nyarugusu.
Wakiliyar HCR a Burundi, Brigitte Mukanga Eno, ta ce fiye da ‘yan gudun hijira 37,000 sun riga sun dawo gida tun farkon wannan shekara. Tun daga Janairun 2017 kuma, sama da mutane 300,000 aka mayar da su Burundi daga kasashen waje.
A kididdigar baya-bayan nan, adadin ‘yan gudun hijirar Burundi ya kai 253,042 zuwa karshen Fabrairu 2026. Tanzania ce ke karbar mafi yawan su da sama da 101,720, sai Rwanda, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Uganda da Kenya.
Wannan babban komawar na da alaka da zaman lafiya da aka samu a kasar bayan rikicin siyasa da ya barke kusan shekaru goma da suka wuce, lokacin da marigayi shugaban kasa Pierre Nkurunziza ya nemi wa’adi na uku, lamarin da ya jawo tashin hankali da gudun hijira.














