Rasha ta ce sojojinta sun taimaka wajen daƙile wani hari da aka kai a filin jirgin saman Diori Hamani International Airport da ke Niamey a makon jiya, harin da ƙungiyar Daesh ta ɗauki alhaki. A cewar Moscow, aikin hadin gwiwa tsakanin dakarun Rasha da sojojin Nijar ne ya dakile harin.
Gwamnatin Nijar ta riga ta bayyana cewa “abokan hulɗa ’yan Rasha” sun taimaka wajen dakatar da harin, lamarin da ya yi sanadin kashe mahara 20 tare da jikkata sojoji huɗu. Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce an cim ma nasarar ne ta hanyar haɗin gwiwar tsaro, tana mai Allah-wadai da abin da ta kira hari na masu tsattsauran ra’ayi.
Hukumomin Nijar sun kuma zargi wasu ƙasashe—ciki har da Benin, Faransa da Ivory Coast—da hannu wajen tallafa wa harin, zargin da ke ƙara tsananta takaddamar siyasa a yankin. Shugaban Nijar, Abdourahamane Tiani, ya ziyarci sansanin sojojin Rasha domin bayyana godiya kan abin da ya kira ƙwarewar aikin.
Rasha na ƙara faɗaɗa tasirinta a yankin Sahel bayan jerin juyin mulki, inda ta tura dakarun tsaro ko masu horaswa zuwa wasu ƙasashen Afirka. Moscow ta ce gudunmawar dakarunta na mayar da hankali ne kan yaƙar ta’addanci da ƙarfafa zaman lafiyar yankin, yayin da Nijar ke ci gaba da fama da barazanar ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a yammaci da kudu maso gabashin ƙasar.
Majiyar Labari: TRT HAUSA














