Shugaban kasar Indiya Narendra Modi da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, inda suka jaddada bukatar gaggauta rage tashin hankali da kuma komawa ga tattaunawa ta diflomasiyya domin tabbatar da zaman lafiya. Modi ya bayyana cewa sun amince da ci gaba da hadin kai tsakanin kasashen biyu domin karfafa kwanciyar hankali a yankin da ma duniya baki daya.
A nasa bangaren, Macron ya ce Faransa da Indiya na aiki kafada da kafada domin rage rikici, yana mai jaddada cewa diflomasiyya ita ce hanya mafi dacewa wajen warware matsalolin yankin. Ya kuma bukaci dakatar da hare-haren da ke lalata ababen more rayuwa na jama’a, musamman bangaren ruwa da makamashi.
Macron ya kara da cewa akwai bukatar tabbatar da tsaro da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa, yana mai kira da a dakatar da fada domin ba da damar samun mafita mai dorewa ta hanyar tattaunawa. Wannan kira ya zo ne a daidai lokacin da yankin ke shiga wani yanayi na ibada da sabuntawa, inda ya dace a kwantar da hankali.
Wannan matsaya na kasashen biyu na zuwa ne yayin da rikici ya tsananta tun bayan harin hadin gwiwar Amurka da Isra’ila kan Iran, wanda ya haddasa mayar da martani daga Iran da hare-hare a kasashe da dama. Hakan ya kara nuna muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa wajen kare fararen hula da kuma tabbatar da tsaron yankin da tattalin arzikin duniya.














