Gwamnatin Guinea-Bissau ta ayyana haramcin duk wani taron manema labarai ko sanarwar jama’a da ba a samu izini ba, kusan makonni shida bayan sojoji sun karɓi ragamar mulki sakamakon juyin mulki bayan zaɓe.
Matakin ya biyo bayan kifar da Shugaba Umaro Sissoco Embalo a ranar 26 ga Nuwamba, lokacin da sojoji suka dakatar da tsarin zaɓe tare da ayyana mulkin soja na wucin-gadi na tsawon shekara guda.
A wata sanarwa da Majalisar Ƙoli ta Soji ta fitar, ta zargi wasu ‘yan siyasa da ƙungiyoyi da shirya tarurruka a asirce domin tayar da tarzoma da rashin biyayya, abin da ta ce na barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Babban Hafsan Sojoji ya jaddada cewa duk wanda ya saɓa wa dokar zai fuskanci hukunci mai tsanani, bisa kundin tsarin mulki na wucin-gadi da aka wallafa a farkon watan Disamba.
Hukumomi sun ce ƙasar na fuskantar mawuyacin yanayin siyasa wanda zai iya rikidewa zuwa rikicin cikin gida, musamman la’akari da tarihin juyin mulki da tashe-tashen hankula da Guinea-Bissau ta sha tun bayan samun ‘yancin kai a 1974.














