Shugaban jam’iyyar Union of Democratic Forces of Guinea (UFDG), Cellou Dalein Diallo, ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Guinea ta dauka na rushe kusan jam’iyyun siyasa 40 bisa zargin karya dokokin da suka shafi ayyukan jam’iyya. A cikin wani sako da ya fitar, ya bayyana matakin a matsayin babban barazana ga dimokuradiyya, yana mai kira ga ‘yan jam’iyya da sauran ‘yan kasar su tashi tsaye domin kare ‘yancin siyasa.
Diallo ya ce Guinea na fuskantar wani lokaci mai muhimmanci a tarihinta, inda ya zargi gwamnati da kokarin kawar da manyan jam’iyyun da ka iya kalubalantar iko. A cewarsa, wannan mataki na iya zama yunkurin kafa wani tsarin siyasa mai kama da jam’iyya guda daya a kasar.
Tsohon Firaministan ya kuma zargi gwamnatin soja da ta karbe iko a shekarar 2021 karkashin jagorancin Janar Mamadi Doumbouya da tauye ‘yancin jama’a da kuma aikata wasu take-take. Ya bukaci ‘yan Guinea da ke son adalci da ‘yanci su hada kai domin dawo da tsarin mulki da kuma tabbatar da ‘yancin jama’a a kasar.














