Wani mummunan hatsari ya faru a jihar Kordofan ta Kudu a ƙasar Sudan bayan da wata ma’adinar zinari ta rushe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane shida, jikkatar wasu 12, tare da makalewar wasu da dama a ƙarƙashin ƙasa.
Kungiyar Sudan Doctors Network ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a garin Abu Jubaiha, inda ma’aikatan hakar ma’adinai suka makale ƙarƙashin duwatsu da laka bayan rushewar ramin. Kungiyar ta bukaci a ƙara ƙaimi wajen aikin ceto da kuma gaggauta ba da kulawar likita ga waɗanda suka jikkata.
Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta ɗauki tsauraran matakan kare lafiyar ma’aikatan hakar ma’adinai, ciki har da:
Kafa ƙa’idojin tsaro,
Horas da ma’aikata,
Yin sa ido akai-akai kan wuraren hakar ma’adinai.
Ta jaddada cewa sakaci da rashin aiwatar da dokoki na jefa rayukan ma’aikata cikin haɗari, tare da neman a hukunta waɗanda ke da alhakin wannan sakaci.
Muhimmancin Hakar Zinari a Sudan
Hakar zinari ta gargajiya tana ɗaukar fiye da mutane miliyan biyu aiki a Sudan, kuma tana samar da kusan kashi 80% na dukkan zinari da ƙasar ke fitarwa. Duk da tsananin haɗarin da ke tattare da aikin, gwamnati na ƙoƙarin tsara shi domin ci gaba da samar da ayyukan yi da kuma samun kuɗin waje.
Tun bayan raba Sudan ta Kudu a 2011, Sudan ta rasa kusan kashi uku cikin huɗu na kuɗaɗen man fetur, lamarin da ya sa zinari ya zama muhimmin ginshiƙi na tattalin arzikinta.














