Gwamnatin Indonesia ta sanar cewa daga 28 ga Maris za ta hana yara ‘yan ƙasa da shekara 16 amfani da kafafen sada zumunta, domin kare su daga haɗurran intanet kamar batsa, cin zarafin yanar gizo, damfara da kuma jarabar amfani da intanet. Ma’aikatar Sadarwa da Harkokin Dijital ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin samar da muhalli mafi aminci ga yara a duniyar dijital.
Ministar sadarwa Meutya Hafid ta bayyana cewa za a rufe duk wani asusun da ke hannun yara ƙasa da shekara 16 a manyan manhajoji da ake ganin suna da haɗari. Daga cikin kafafen da za su shafa akwai YouTube, TikTok, Facebook, Instagram, Threads, X, Bigo Live da Roblox.
Matakin na cikin sabuwar dokar gwamnati mai suna PP Tunas (Regulation No.17 na 2025), wadda ta tilasta wa kamfanonin fasaha da ke aiki a Indonesia su samar da tsarin tabbatar da shekaru da kuma ƙarin kariya ga yara.
Indonesia ta shiga jerin ƙasashen da ke ƙoƙarin takaita amfani da kafafen sada zumunta ga yara. Kasashe kamar Australia, Faransa da Spain ma sun fara ko suna shirin aiwatar da irin wannan doka domin rage haɗurran da yara ke fuskanta a intanet.














