Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya bukaci kasashen duniya su dauki matakin dakile rikicin da ke kara tsananta a Gabas ta Tsakiya. Wannan na zuwa ne bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai kan Iran da kuma ramuwar gayya da Tehran ta mayar.
Da yake magana a Geneva, Turk ya nuna damuwa kan karuwar hare-haren bama-bamai, kalaman tada hankali, da kuma lalata yankunan fararen hula.
Turk ya ce akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu hare-hare sun shafi makarantu da sauran wuraren fararen hula, yana jaddada muhimmancin mutunta dokokin jin kai na kasa da kasa.
Ya kuma yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa, a fili kuma ba tare da son rai ba kan duk wani zargi na keta doka, yana mai nuni da cewa Amurka ta sanar da fara bincike kan wasu daga cikin wadannan abubuwa.
Ya kara da cewa karin tashin hankali ta hanyar karfin soja ba zai kawo mafita ba, don haka ya bukaci dukkan bangarorin su koma teburin tattaunawa domin neman mafita ta diflomasiyya.
Turk ya kuma nuna damuwa kan halin da ake ciki a Lebanon, inda umarnin barin gidaje bayan hare-haren Hezbollah kan Isra’ila da martanin Isra’ila ya tilasta wa daruruwan dubban mutane tserewa daga gidajensu.
Bugu da kari, ya yi gargadi kan amfani da sabbin fasahohi a yakin zamani, musamman na’urar artificial intelligence, yana mai cewa dole ne duk wani amfani da irin wadannan fasahohi a makamai ya kasance karkashin kulawar dan Adam domin kiyaye ka’idojin kare hakkin bil’adama na duniya.













