An nada Alireza Arafi a matsayin mamba a Majalisar Jagoranci ta Iran kuma wanda zai jagoranci majalisar na wucin-gadi kafin a naɗa wanda zai gaji Ali Khamenei, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ISNA ya ruwaito.
A matsayinsa na malamin addini kuma mamba a Majalisar Shura ta Iran, Arafi zai kasance cikin Kwamitin Jagoranci na wucin-gadi tare da Shugaba Masoud Pezeshkian da Babban Alkali Gholamhossein Mohseni Ejei.
Nadawar Arafi ta zo ne bayan an kashe Babban Jagoran Iran, Ali Khamenei, a hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai, abin da ya ja Sojojin Juyin Juya Hali na Iran suka lashi takobin ɗaukar fansa.
Gidan talabijin na gwamnati a ƙasar a ranar Lahadi ya sanar da zaman makokin kwanaki 40 da kuma hutu na kwanaki bakwai ga jama’a bayan mutuwar babban jagoran ƙasar mai shekaru 86, wanda yake riƙe da madafun iko tun 1989.
A gefe guda, Sojojin Juyin Juya Hali na Iran sun yi alƙawarin hukunta “maharan” Khamenei.
An ruwaito cewa an kuma kashe ‘yarsa, mijin ‘yarsa da jikarsa a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai.
Tun a ranar Asabar, Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu suka bayyana Khamenei ya “rasu”.
Hari kan jagoran Iran lokacin da ya yake ganawa da ƙusoshin ƙasar
An tsara harin da Isra’ila da Amurka suka kai a ranar Asabar a daidai lokacin da ake cewa Khamenei yana taro tare da manyan mataimakansa.
Isra’ila ta ce an kashe Khamenei tare da manyan mataimaka, ciki har da Ali Shamkhani, tsohon sakataren Majalisar Tsaron Kasa mai karfi, da Mohammad Pakpour, kwamandan Rundunar Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC).
Wasu majiyoyi sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Khamenei ya gana a ranar Asabar da Shamkhani da Ali Larijani a wani wuri mai tsaro jim kadan kafin a fara kai hare-haren.














