Sojojin Iran sun ƙaddamar da abin da kafafen watsa labaran gwamnati suka bayyana a matsayin babban harin makami mai linzami da jirage marasa matuƙa waɗanda suka faɗa kan “sansanonin abokan gaba” a faɗin yankin, inda suka ƙona tankunan mai da ma’ajiyar harsasai a sansanin sojin sama na Prince Hassan a Jordan.
Rundanar Juyin Juya Halin Iran ta IRGC ta ce harin a kan wannan sansanin na Jordan shi ne mataki na farko na martaninta ga hare-haren Amurka kan sansanonin bakin teku na Iran, inda ta yi gargaɗin cewa za ta ci gaba aikin ramuwar gayya.
IRGC ɗin ta ce sojojin samanta sun kuma kai hari kan sansanin sojin sama na Sheikh Isa a Bahrain, inda ta ce ta kai hari kan wuraren gyaran helikopta, garejin da ake adana jirgin P-8 da cibiyar umarni da iko ta jiragen sama marasa matuka na Amurka.
Kafafen watsa labaran gwamnati na Iran sun ruwaito cewa IRGC ta kai hari filayen jirage biyu a Kuwait. Ikirarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin hare-haren ramuwar gayya tsakanin Iran da Amurka a faɗin yankin.
Ta ƙara da cewa ta kai harin ne bayan ta gano wuraren da kuma sa ido kan “motsin abokan gaba” a cikin awanni 48 da suka gabata.
A wata sanarwa, IRGC ta ce harin rundunar ta ruwa a cikin tashar Hormuz ya faɗa ne kan jirage biyu waɗanda ake zargi da kashe na’urar bin diddiƙinsu (tracker), karya ka’idojin zirga-zirgar ruwa da zama barazana ga tsaron ruwa.
“Halastaccen wuri na kai hari”
Hakan ya biyo bayan gargadin da Iran ta a yi ranar Litinin kan cewa duk wani wuri da aka yi amfani da shi wajen kaddamar da hare-hare kan kasar za a dauke shi a matsayin “halastaccen wuri na kai hari” don ramuwar gayya.
A wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen ta gargadi kasashen makwabta da su hana a yi amfani da yankunansu ko wuraren su na gwamnati da Amurka ko wasu bangarori wajen kai hari kan Iran.
Ta ce kasashen makwabta na da alhaki karkashin doka ta kasa da kasa hana a yi amfani da yankunansu wajen ayyukan soja kan Iran, tare da sake jaddada cewa “duk wani wurn da aka ƙaddamar” da hari zai zama wurinm da Iran za ta kai wa farmaki.
Wannan ci gaba ya zo ne bayan ‘yan sa’o’i da rundunar sojin Amurka ta sanar da sabon zagaye na hare-hare kan Iran, inda ta ce aikin yana nufin rage ikon Tehran na kai hari kan jiragen ruwan kasuwanci a Mashigar Hormuz.
Ma’aikatar ta yi tir da hare-haren Amurka da aka kai a cikin awanni 22 da suka gabata, sannan ta bayyana su a matsayin babban take hakkin Kundin Majalisar Dinkin Duniya.
Ta zargi Washington da karya kusan dukkan sassa na yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a kwanaki 25 da suka wuce da kuma aikata “laifukan yaƙi” ta hanyar kai hari kan ababen more rayuwa na sufuri, kamun kifi, jiragen kaya da cibiyoyin nazarin yanayi.

















