Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Isra’ila ta fara amfani da tsoffin makamai marasa inganci sosai a yakin da take yi da Iran. Tashar talabijin ta gwamnati KAN ta ce ana amfani da makaman da aka ajiye tun kusan rabin karni domin kai hare-hare kan sansanonin soji a Iran.
A cewar rahoton, an dauki wannan mataki ne domin rage kudin yaki da kuma fitar da tsoffin makaman da suka dade a ajiya. An kuma ce an gano amfani da wadannan makamai ne kwatsam a baya-bayan nan, yayin da ma’aikatar tsaron Isra’ila ba ta yi wani karin bayani ba kan lamarin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin yankin ke kara kamari tun bayan harin hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu. Harin ya jawo asarar rayuka da dama tare da tada martanin Iran ta hanyar kai hare-haren jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami.
Hare-haren ramuwar gayya daga Iran sun shafi Isra’ila da wasu kasashen yankin da ke dauke da sansanonin Amurka, lamarin da ya janyo asarar rayuka, lalacewar ababen more rayuwa da kuma girgiza kasuwannin duniya da zirga-zirgar jiragen sama.














