Rahoton da The New York Times ya wallafa ya ce Shugaban Donald Trump na duba yiwuwar kai wani hari na soji da aka takaita kan Iran, tare da yiwuwar faɗaɗa matakin idan tattaunawar diplomasiyya ta gaza. A cewar jami’an Amurka da jaridar ta ambato, an ce Trump ya nuna cewa zai iya ɗaukar matakai masu tsauri idan Tehran ba ta janye shirinta na nukiliya ba.
Ana sa ran masu tattaunawa daga Amurka da Iran za su gana a Geneva, a wani yunkuri na kauce wa rikicin soji. Tattaunawar, wadda Oman ke shiga tsakani, ta biyo bayan zaman da aka yi a Muscat da Geneva. Rahoton ya ce ana la’akari da wuraren da za a iya kai hari, ciki har da cibiyoyin nukiliya da na soji.
Trump ya jaddada cewa duk wata yarjejeniya dole ta kai ga “zero enrichment”, amma Iran ta ce ba za ta amince da hakan ba. Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce ƙasarsa na da haƙƙin samar da makamashin nukiliya a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
A lokaci guda, European Union ta yi kira ga mafita ta diplomasiyya. Babbar jami’ar harkokin wajen EU, Kaja Kallas, ta ce yankin ba ya buƙatar sabon yaƙi, tana mai ƙarfafa tattaunawa maimakon tashin hankali.
Majiyar Labari: TRT WORLD














