Sojojin Isra’ila sun kai sabbin hare-haren sama a unguwar Dahiye da ke birnin Beirut, babban birnin Lebanon. Rahotanni sun ce jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare da dama tun daga safiyar Laraba, inda aka ji karar fashewar abubuwa tare da ganin hayaki mai yawa yana tashi daga yankin.
Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa hare-haren sun nufi wuraren da suke da alaka da kungiyar Hezbollah, wadda ke da karfi a yankin Dahiye. Harin ya zo ne bayan da Isra’ila ta yi ikirarin cewa an harba makamai masu linzami daga Lebanon zuwa arewacin kasarta.
Rikicin tsakanin bangarorin biyu ya kara tsananta a ‘yan kwanakin nan, inda Isra’ila ta fadada hare-haren sama da kuma ayyukan soji a Lebanon. Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce akalla mutane 50 sun mutu sakamakon hare-haren da aka kai a sassa daban-daban na kasar.














