Jami’an tsaron Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda aƙalla 21 a wani samame da aka gudanar a dajin Shawu da ke Jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya. kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Asabar.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasiru Muazu, ya ce an gudanar da wannan samame ne a ƙarƙashin aikin “Forest Sanity III” a yankin Faskari na jihar.
Muazu ya bayyana cewa an kashe ‘yan ta’adda 21, yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka. Haka kuma, jami’an tsaro sun ƙwace babura guda 40 da kuma adadi mai yawa na alburusai a yayin samamen.
Nijeriya na fama da matsalar ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane da kuma ƙungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da ISWAP (reshen Daesh na Afirka ta Yamma), musamman a yankin arewa.
Duk da cewa akwai hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, yin garkuwa don neman kuɗin fansa ya ci gaba da zama ruwan dare a Nijeriya. Ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai kan kai hari kan ƙauyuka, makarantu da matafiya don neman kuɗin fansa.














