Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta gudanar da taron bankwana don murnar kammala sanin makamar aiki na shekara guda da daliban likitanci ‘yan kasar Somalia su 23 suka yi a jami’ar.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Ahmed ne ya jagoranci bikin da aka gudanar a Babban Dakin Taron Sanatocin Jami’ar.
Taron ya samu halartar Mai Girma Jamal Barrow, Jakadan Somalia a Nijeriya, wanda shi ne Babban Bako na Musamman.
Wadannan ne rukuni na farko na daliban likitanci na Somalia da aka horar a kwalejin aikin likitanci ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, bayan Yarjejeniyar Fahimtar Juna da aka sanya hannu a kai tsakanin ABU da Jami’ar SIMAD ta Mogadishu a watan Fabrairun 2024.
Da yake jawabi a wajen taron, Jakada Barrow ya bayyana bikin yaye daliban a matsayin lokaci na alfahari da Somalia da Nijeriya, yana mai nuna muhimmancin hadin kai a fannin ilimi a matsayin babban jigon alakar kasashen biyu.
“Baya ga yarjeniyoyin siyasa da musayar diflomasiyya, mutane ne ke gina gada mafi karfi a tsakanin kasashe – musamman ma matasa – da suke musayar ilimi, al’adu da kwarewar rayuwa,” in ji shi.
Ya yi tsokaci da cewa daliban da suka samu horon ba ilimin likitanci kawai suka samu ba, har da ma koyon al’adu da jin su ma na Nijeriya ne, wanda hakan zai karfafa musu wajen inganta kula da lafiya a Somalia.
Jami’in diflomasiyya ya taya daliban murna bisa nasarar da suka samu, inda ya kuma bukaci da su yi aiki da nasarar a matsayin bajon girma a yayin da suke sauke nauyin da ke kan su a gida.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Jami’ar ta ABU da ke Zaria a Nijeriya Farfesa Adamu Ahmed ya sake jaddada aniyar ABU wajen bayar da goyon baya ga ‘yan uwan cibiyoyin ilimi na Afirka, inda ya kuma yaba wa jami’ar SIMAD saboda zabar ABU da ta yi don horar da daliban likitocinta.
Ya yi wa daliban maraba tare da yin alkawarin jami’ar za ta ci gaba da ba su goyon baya a yayin da suke ayyukansu a Somalia.
Shi ma da yake jawabi a wajen, shugaban tsangayar nazarin likitanci ta jami’ar Farfesa S. Shehu ya ce wannan ne karo na farko da aka fara bayar da horon, kuma dukka masu sanin makamar aikin sun samu horo da jarrabawa, kuma za su karbi shaida kammalawa.
Shugaban Jami’ar SIMAD Abdikarim Mohaidin Ahmed a nasa jawabin ya bayyana godoyarsu ga Jami’ar ABU bisa karbar bakuncin dalibansu, inda ya kuma yaba wa Jakada Barrow saboda jajircewarsa.
Hadin kan ya zama wani mataki mai matukar muhimmanci a fannin karfafa hadin gwiwa a fannin ilimi tsakanin Nijeriya da Somalia, inda ake samarwa da rainon kwararrun kula da lafiya da za su hidimtawa al’ummunsu.














