Amurka Nijeriya Tsaro

Jiragen Amurka Sun Fara Leken Asiri a Samaniyar Nijeriya Bayan Barazanar Trump

Amurka na gudanar da jiragen leken asiri a samaniyar Nijeriya a wani yunƙuri na ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro, a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsanancin matsalar tsaro bayan barazanar Trump kan tsoma bakin soji.

Newstimehub

Newstimehub

23 Dec, 2025

2025 12 18t211224z 1217044859 rc26jiai88jw rtrmadp 3 usa caribbean military buildup main e1766504123296

Tun daga ƙarshen watan Nuwamba, wasu jiragen saman Amurka na shawagi a sararin samaniyar Nijeriya, suna gudanar da ayyukan leken asiri da tattara bayanai. Wannan na zuwa ne a wani yanayi da ya jawo hankalin masana tsaro, musamman ganin cewa hakan ya faru jim kaɗan bayan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na iya tura sojoji Nijeriya.

Rahoton Reuters ya nuna cewa bayanan bin diddigin jiragen sama da kuma bayanan jami’an Amurka na yanzu da tsoffi sun tabbatar da cewa ana gudanar da ayyukan ne domin leken asiri da tattara bayanai a manyan sassan Nijeriya. Sai dai Reuters ta ce ba ta iya tantance irin bayanan da ake nema ba.

Bayanan sun kara da cewa jiragen, waɗanda kamfanin kwangila na Amurka Tenax Aerospace ke sarrafawa, na tashi ne daga Ghana, su ratsa sararin samaniyar Nijeriya kafin su koma Accra. Ana amfani da irin wadannan jirage ne wajen sa ido da tattara bayanan tsaro tare da haɗin gwiwa da sojojin Amurka.

Majiyar Labari: Trt Hausa