Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya da ke zama a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar Abubakar Malami, tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Tsohon Ministan Shari’a, na neman beli, bayan tsare shi da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa EFCC ta yi.
A cikin hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai Shari’a Babangida Hassan, wanda ke jagorantar shari’ar, ya bayyana cewa tsare Malami yana bisa doka kuma yana tsare ne bisa umarnin kotu.
Malami, wanda Babban Lauya ne na Nijeriya (SAN), ya garzaya kotu ta hannun lauyansa Sulaiman Hassan, inda ya bayar da hujjar cewa ci gaba da tsare shi da EFCC ke yi yayin da ake gudanar da bincike abu ne da ya saɓa wa doka tare da take masa haƙƙinsa na kundin tsarin mulki na ‘yancin kai.
Sai dai EFCC ta bijire wa wannan buƙata, tana mai jaddada cewa ana tsare Malami ne bisa sahalewar da aka samu daga wata kotun ta daban da ke Abuja.
J.S. Okutepa, wanda shi ne lauyan EFCC, ya shaida wa kotu cewa Mai Shari’a S.C. Oriji ne ya bayar da umarnin tsarewar da kuma bin tsarin dokar shari’ar manyan laifuka ACJA
Okutepa ya ce hukumar ta yi aiki ne cikin iyakar doka, kuma ba za ta tsare wani da ake zargi fiye da lokacin da kotu ta amince ba.
A hukuncinsa, alkali ya goyi bayan matsayar EFCC, yana mai nuna cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya da tsarin dokar shari’ar manyan laifuka ACJA suna amince da tsare mutum bisa sahihin umarnin da aka samu na tsarewa da kotu mai hurumi.
Alkalin ya yanke hukuncin cewa buƙatar da aka gabatar a gabansa tana da tangarda ta fuskar tsarin shari’a, domin a zahiri tana neman kotun ta sake duba ko ta soke umarnin da wata kotu mai matsayi ɗaya ta bayar.
“Yarda da wannan buƙata zai zama kamar wannan kotu na zama kotun ɗaukaka ƙara a kan hukuncin wata kotu mai matsayi ɗaya,” in ji Hassan, yana mai ƙara da cewa irin wannan mataki ya wuce ikon kotun.














