Kotun Koli ta India ta amince da cire na’urar da ke tallafa wa rayuwar wani matashi mai shekara 32 wanda ya shafe sama da shekaru 12 yana cikin yanayin vegetative state. Wannan shi ne karon farko da kotun ta bayar da izini ga irin wannan mataki na passive euthanasia a ƙasar.
Alkalai biyu, J. B. Pardiwala da K. V. Viswanathan, ne suka duba bukatar da mahaifin marar lafiyar, Harish Rana, ya shigar. Iyalin sun bayyana cewa tun bayan hatsarin da ya same shi a 2013, an dade ana riƙe shi da rai ta hanyar na’urorin tallafi kawai.
Rana, wanda ya fito daga jihar Uttar Pradesh a arewacin India, ya samu munanan raunukan kai bayan wani gini ya rushe a kansa shekaru da dama da suka wuce. Tun daga lokacin yake cikin koma mai tsanani ba tare da wata alamar dawowa cikin hayyaci ba.
A hukuncin da kotun ta yanke ranar Laraba, an amince a cire na’urar tallafin rayuwa da kuma dakatar da ciyar da shi ta hanyar na’ura (clinically assisted nutrition). Tun a 2018, Kotun Koli ta riga ta yanke hukunci cewa ana iya janye tallafin rayuwa ga marasa lafiya da ke cikin koma mara magani, tana mai cewa mutum na da ‘yancin mutuwa cikin mutunci.














