Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan wata takarda da ke nuna aniyar janye ƙasar daga ƙungiyoyi da dama na ƙasa da ƙasa, ciki har da wasu hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), a cewar Fadar White House.
Sanarwar da aka fitar a ranar Laraba ta ce shirin ya shafi jimillar ƙungiyoyi 66—ciki har da ƙungiyoyi 31 na MDD da 35 da ba na MDD ba—da gwamnatin Trump ta ce ba sa biyan buƙatun Amurka.
Fadar White House ta bayyana cewa ba za ta fitar da jerin sunayen ƙungiyoyin ba, amma ta zarge su da yaɗa manufofin sauyin yanayi masu tsauri, ra’ayin shugabanci na duniya, da aƙidu da ke saɓa wa ikon siyasa da tattalin arzikin Amurka. A cewarta, matakin ya biyo bayan cikakken bita da aka yi kan dukkan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, manyan tarukan ƙulla ƙawance da yarjejeniyoyin da Amurka ke ciki.
Gwamnatin Trump ta ce janyewar za ta kawo ƙarshen biyan tallafi da kuɗaɗen haraji ga ƙungiyoyin da ke fifita manufofin duniya fiye da bukatun Amurka, tare da mayar da waɗannan kuɗaɗen zuwa ayyukan da gwamnati ta ce sun fi dacewa da muradun ƙasar.
Tun fara wa’adinsa na biyu, Trump ya dauki matakai da suka haɗa da rage tallafin Amurka ga MDD, dakatar da hulɗa da Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta MDD, tsawaita dakatar da tallafin UNRWA, ficewa daga UNESCO, da kuma sanar da shirin ficewa daga Hukumar Lafiya ta Duniya da yarjejeniyar yanayi ta Paris.














