A wani muhimmin lamari na siyasa, María Corina Machado, shugabar adawa a Venezuela da kuma mai nasarar Nobel Peace Prize na 2025, ta yi wata gagarumar alama ta godiya lokacin da ta gabatar da lambar kyautar zaman lafiya ga Donald Trump, tsohon Shugaban Amurka, a White House.
Machado ta ce ta gabatar da lambar ne don nuna godiya bisa yadda Trump ya taka rawa a kan ‘yancin ‘yan Venezuela da kuma kokarin kawo canji bayan rundunar Amurka ta kama Maduro a farkon wannan watan.
A jawabin da Machado ta yi wa ‘yan jarida bayan taron, ta bayyana cewa lambar ta kasance matsayin godiya ga Trump saboda “taimakon da ya bayar wajen samun ‘yanci,” duk da cewa Kungiyar Nobel ta sanar da cewa lambar ba za a iya sauyawa ko mika mata ga wani ba.
Trump ya amince da kyautar, inda ya rubuta a dandalin sa na Truth Social cewa alan ya kasance babban girmamawa gare shi kuma ya godewa Machado kan wannan alheri.
Tun kafin haka, Hukumar Nobel ta yi karin haske cewa lambar zaman lafiya ba za a iya rabawa ko mika ta ba koda Machado ta yi nufin yin hakan.














