Nigerian Senate ta sanar da shirya zaman gaggawa ba tare da bayyana dalili ba, a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan batun tura sakamakon zabe ta lantarki. A sanarwar da Magatakardar Majalisar, Emmanuel Odo, ya fitar, an umarci sanatoci su hallara a ginin Majalisar Ƙasa bisa umarnin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ranar Talata 10 ga Fabrairu, 2026 da karfe 12 na rana.

Ko da yake ba a bayyana dalilin kiran taron ba, lamarin na zuwa ne bayan Majalisar ta amince da kudurin gyaran Dokar Zabe zuwa karatu na uku, inda aka bar tanadin tura sakamako ta lantarki kamar yadda Dokar 2022 ta tanada. Majalisar ta ki amincewa da bukatar wajabta tura sakamako kai tsaye (real-time), tare da watsi da shawarar haramta sayen kuri’u na tsawon shekaru goma, tana barin hukuncin daurin kurkuku da tara.
Tun bayan hakan, Majalisar ta fuskanci suka daga jama’a da kungiyoyi, sai dai wasu sanatoci sun kare matakin. Sanatan Anambra ta Tsakiya, Victor Umeh, ya ce fiye da kashi 85 cikin 100 na sanatoci sun amince da tura sakamako ta lantarki gaba ɗaya, kuma abin da aka cire kawai shi ne kalmar “real time” saboda damuwar matsalolin sadarwa a wasu yankuna.
Umeh ya kara da cewa rudani ya samo asali ne lokacin zaman Majalisar, inda aka yi yunƙurin sauya kalmar “transmission” zuwa “transfer” ba tare da muhawara ba. A cewarsa, batun tura sakamako bai taba zama abin gardama ba, domin an riga an tattauna shi dalla-dalla a zaman sirri na Majalisar.














