Mataimakin shugaban Kwamitin Tsaron Rasha, Dmitry Medvedev, ya yaba wa Shugaban Amurka Donald Trump a matsayin shugaba mai tasiri da ke neman zaman lafiya, amma ya ce Moscow ba ta ga wata shaida ta jiragen ruwa masu dauke da makaman nukiliya da Trump ya ce ya matsar kusa da gabar Rasha ba. Medvedev ya bayyana hakan ne yayin wata hira, yana mai cewa Trump na son a tuna da shi a tarihi a matsayin mai sasanta rikici, musamman kan yakin Ukraine.
Medvedev ya ce Amurkawa ne suka zabi Trump, kuma Rasha na girmama wannan zabin, yana mai karyata rade-radin cewa Trump yana aiki ne don Rasha. Ya kara da cewa duk da yadda ake kallon Trump a matsayin mai hargitsi, a zahiri yana tafiyar da tsari mai ma’ana da kuma tunani na kasuwanci, lamarin da ya sa tattaunawa da Amurka ta fi zama mai amfani a baya-bayan nan.
Dangane da ikirarin Trump na watan Agusta cewa ya umarci jiragen ruwa masu nukiliya biyu su matsa kusa da Rasha, Medvedev ya yi barkwanci yana cewa har yanzu ba su gano inda jiragen suke ba. Ya ce fahimtar Trump na bukatar a duba asalinsa na dan kasuwa, yana nuni da cewa ba a daina zama dan kasuwa ko da bayan shiga siyasa.
Medvedev ya kuma ce Rasha na sa ran samun nasarar soji a yakin Ukraine nan ba da jimawa ba, amma ya jaddada cewa abu mafi muhimmanci shi ne hana sake barkewar wani sabon rikici. Ya ce burin nasara ba wai kawai cin yaki ba ne, illa tabbatar da zaman lafiya na dogon lokaci bayan rikicin.
Majiyar Labari: REUTERS














