Gwamnatin Mozambique ta yi kira ga al’ummar duniya da su gaggauta kai taimakon jin-ƙai bayan ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru masu yawa ta raba daruruwan dubban mutane da muhallansu tare da lalata muhimman ababen more rayuwa a ƙasar.
Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa (INGD) ta ce ambaliyar ta fi kowace tsanani cikin shekaru aru-aru, inda alkaluma suka nuna cewa fiye da mutane 600,000 sun rasa muhallansu a jihohin Gaza, Zambezia, Inhambane da Sofala. An ce kusan kashi 40 cikin 100 na lardin Gaza yana ƙarƙashin ruwa.
Mataimakin shugaban INGD, Gabriel Monteiro, ya bayyana cewa albarkatun ƙasar ba su isa ba domin tinkarar bala’i mai girma haka, yana mai kira ga duniya da ta kawo ɗauki.
“Abin da muke fuskanta ya wuce duk wani shiri da muka tanada. Don haka muna roƙon agajin jin-ƙai daga ko’ina a duniya domin rage illar wannan ambaliya,” in ji shi.
Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane 13, yayin da ake ci gaba da neman wasu da suka ɓace. UNICEF ta yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu, musamman yara, na iya ƙaruwa.
Gwamnatocin Afirka ta Kudu da Birtaniya sun tura sojoji domin taimakawa aikin ceto, yayin da dubban mutane ke fuskantar ƙarancin matsuguni, ruwa, abinci da tsafta.














