Yayin da kwanaki 21 kacal suka rage, birnin Legas na shirin karɓar dubban ’yan gudun fanfalaki daga sassa daban-daban na duniya a gasar Access Bank Lagos City Marathon 2026, wadda za a gudanar a ranar Asabar, 14 ga Fabrairu. Wannan gasar, wadda ita ce ta 10 a tarihi, ana sa ran za ta fi dukkan shekarun baya armashi da kayatarwa.
A karo na farko tun kafa gasar, an gabatar da sabon tsarin hanya mai tsawon kilomita 42. Gudun zai fara ne daga ORCA Mall a Victoria Island, ya ratsa sassan Lagos–Calabar Coastal Road, sannan ya ƙare a Eko Atlantic City – ɗaya daga cikin fitattun wuraren zamani a Afirka.
Gasar na ɗaya daga cikin manyan tseren duniya da ke da World Athletics Gold Label, kuma manyan ’yan wasa daga Kenya, Ethiopia da Uganda za su fafata da zakakuran ’yan Najeriya da ke son ɗaukar kambu a gida. Ana sa ran za a ga gasa mai zafi tsakanin manyan kasashen Afirka masu tarihi a fagen gudu.
Baya ga ƙwararru, dubban masu gudu na nishaɗi ma za su shiga, lamarin da zai mayar da titunan Legas tamkar babban filin bukin wasanni, lafiya da haɗin kan al’umma.
An sanar da cewa rajista na ci gaba har zuwa 31 ga Janairu, don bai wa masu sha’awar shiga damar kammala rajistarsu kafin ranar gasar.














