Kungiyar Likitocin Masu Yi wa Kansu Horaswa ta Najeriya (NARD) ta sanar da shirin dawo da yajin aikin kasa baki daya daga ranar 12 ga Janairu, 2026, sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.
Kungiyar ta ce yajin aikin, wanda ta lakaba masa suna “No Implementation, No Going Back,” zai fara ne da misalin karfe 12 na daren Litinin idan gwamnati ba ta biya bukatunsu ba.
Wannan mataki ya biyo bayan taron gaggawa na shugabannin kungiyar, inda suka ce gwamnati ta saba alkawuran da ta dauka tun bayan janye yajin aikin da aka dakatar a watan Nuwamba.
NARD ta bukaci mayar da likitocin da aka sallama, biyan hakkokin albashi da alawus, da kuma warware batutuwan da suka shafi ma’aikata kafin ta sake duba batun janye yajin aikin.














