A wani rahoto da ke nuna irin tsananin yaƙin da Nijeriya ke yi da safarar miyagun ƙwayoyi, Hukumar NDLEA ta bayyana gagarumar nasara da ta samu cikin shekaru biyar, inda ta katse hanyoyin masu fataucin ƙwayoyi tare da kama dubban mutane da ƙwace tarin miyagun abubuwa, abin da ya kara nuna cewa ƙasar ba za ta zama mafakar laifi ba.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, ya ce daga cikin shekaru biyar da suka wuce, hukumar ta kama mutum 77,792 tare da ƙwace kilo 14,847 na miyagun ƙwayoyi. Ya ce an kuma kama manyan jagororin fataucin ƙwayoyi 128, yayin da kotuna suka yanke wa mutane 14,225 hukuncin dauri.
A bangaren gyaran hali, sama da masu shan ƙwayoyi 32,000 sun amfana da shirin warkarwa, yayin da aka gudanar da dubban shirye-shiryen wayar da kai a faɗin ƙasar. Marwa ya danganta nasarorin da ingantaccen tattara bayanan sirri, haɗin gwiwa da hukumomi, da kuma sake fasalin NDLEA domin ƙara inganci.













