Nijeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) na shirin ɗaga alaƙar tattalin arzikinsu zuwa wani sabon matsayi ta hanyar rattaba hannu kan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Tattalin Arziki (CEPA) a birnin Abu Dhabi. Ana sa ran yarjejeniyar za ta kammala ne yayin ganawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaban UAE, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, a gefen taron Abu Dhabi Sustainability Week.
Da zarar an sanya hannu, yarjejeniyar za ta samar da tsari na doka da kariya ga kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen biyu, tare da buɗe ƙofofi ga sabon jari da ake hasashen zai haura dala biliyan 10, musamman a fannonin makamashi, noma, masana’antu da gine-gine.
Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, ya ce yarjejeniyar na da matuƙar muhimmanci wajen bai wa ‘yan kasuwa kariya da kuma ƙarfafa amincewar masu zuba jari daga UAE. Ya bayyana cewa makamashi, musamman ayyukan gas don samar da wutar lantarki, na daga cikin ginshiƙan haɗin gwiwar, ganin yadda Nijeriya ke da dimbin iskar gas da ba a yi amfani da ita yadda ya kamata ba.
Baya ga haka, CEPA za ta ƙarfafa cinikayyar kayan noma da masana’antu, da kuma bunƙasa alaƙa a bangaren kuɗi, sufuri da jiragen sama. Gwamnatin Nijeriya ta ce taron Abu Dhabi Sustainability Week na ba da dama wajen jawo kuɗaɗe don ayyukan sauyin yanayi da ci gaban tattalin arziki.
A shekarar 2024, Nijeriya da UAE sun riga sun kulla yarjejeniyoyin zuba jari 14 da darajarsu ta kai dala biliyan 5, tare da sa hannu kan yarjejeniyar ilimin dijital domin horar da matasan Nijeriya, alamar ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen biyu.














